Ministan Harkokin Wajen Biritaniya Na Ran Gadi A Afrika
Ministan harkokin wajen kasar Biritaniya, Boris Johnson, na ziyara a Banjul fadar gwamnatin Gambia.
A yayin da yake ganawa da sabon shugaban kasar ta Gambia, Mista Johnson, ya bawa gwamnatin Adama Barrow akan matakinta na neman dawowa cikin kungiyar Commonwealth ta kasashe galibi 'yan renon Ingila ciki har da Gambia.
Haka kuma Biritaniya ta sha alwashin taimakuwa sabuwar gwamanatin Gambia dangane da matakinta na aiwatar da sauye-sauye a fannin shari'a.
Wannan ziyara ta Mista Johnson, ita ce ta farko ga wani ministan harkokin wajen Biritaniya a Gambia, tun bayan samun yancin kanta daga turawa 'yan mulkin mallaka na Biritaniya a shekara 1965.
Baya ga kasar Gambia a yau ne ake sa ran M. Johnson zai isa Ghana inda cen din ma zai gana da sabon shugaban kasar, Nana Akufo-Addo wanda ya yi rantsuwar kama aiki a ranar bakwai ga watan Jiya.