Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana fatanta na gyaruwar Al'amura a kasar Somaliya
(last modified Wed, 15 Feb 2017 17:55:18 GMT )
Feb 15, 2017 17:55 UTC
  • Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana fatanta na gyaruwar Al'amura a kasar Somaliya

Kungiyar Tarayyar Afirka ta bukaci sabuwar Gwamnatin Somaliya da ta gudanar da gyara a tsarin Ma'aikatun kasar tare kuma da kawo sauki a rayuwar Al'umma.

Kamfanin dillancin Labaran Xin Huwa na kasar China ya nakalto Francisco Madeira wakilin kungiyar AU a kasar Somaliya na cewa bayan dage zaben Shugaban kasa har so biyar a Somaliya, shakka babu kasar ta fuskanci matsaloli da dama kafin gudanar da wannan zabe, domin haka wajibi ne ga sabuwar Gwamnatin kasar ta himmatu wajen ci gaba da kuma kyautata rayuwar Al'ummar kasar.

Mista Madeira ya kara da cewa Sabon Shugaban kasar  Muhamad Abdul...Farmajo nada babban kalu bale a gare shi musaman ma wajen tabbatar da tsaro, yaki da fasadi a Ma'aikatun Gwamnatin kasar gami da tabbatar da sulhu tsakanin Al'ummar kasar.

A yayin da ya koma kan aiyukan ta'addanci na kungiyar Ashabab, wakilin Kungiyar Tarayar Afirkan ya bayyana cewa babban abinda ya kamata sabuwar Gwamnatin ta sanya a gaba, kawo gyara a cibiyoyin tsaron kasar kama daga Ma'aikatar 'yan sanda , Ma'aikatar Leken asiri zuwa ga bangaren Sojojin kasar wanda hakan shi zai sanya a ci nasara wajen tabbatar da tsaro a fadin kasar baki daya.