Adawar Kotun Kolin Masar da rusa Jam'iyar Annor
Babbar Kotun kolin Masar ta bayyana adawar ta da rusa Jam'iyar Annor ta salafiyawa
Kafar watsa labaran Alhayat ta birnin Landon ta habarta cewa Babbar kotun kasar Masar ta yi watsi da bukatar wasu Mutane na rusa Jam'iyar Annor da kuma wasu Jam'iyun siyasa na daban.Katon ta ce bukatar da Taufik Okasha tsohon Dan Majalisar kasar ya gabatar na rusa dukkanin Jam'iyun Siyasar da aka kafa bayan Juyin milki na ranar 25 ga watan Janairu, abu ne da ya sabawa kundin tsarin milkin kasar dan haka kotun ta yi watsi da wannan bukata.
A cewar Tsohin Dan Majalisar Dokokin kasar, wadannan Kungiyoyin Siyasa sun ki halartar al'amuran Siyasar kasar kuma babu wata rawa da suka taka da zaben 'yan Majalisun Dokokin kasar.