An karya lagon boko haram a najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17922-an_karya_lagon_boko_haram_a_najeriya
Babban hafsan sojin Najeriya ya ce bayan kafa Rundunar hadin gwiwa na kasashen yankin tabkin Tchadi, an samu nasarar raunana mayakan boko haram
(last modified 2018-08-22T06:59:43+00:00 )
Feb 22, 2017 07:32 UTC
  • An karya lagon boko haram a najeriya

Babban hafsan sojin Najeriya ya ce bayan kafa Rundunar hadin gwiwa na kasashen yankin tabkin Tchadi, an samu nasarar raunana mayakan boko haram

A yayin buda taron manyan hafsoshin soja na kasashen yankin tekun Tchadi (LCBC) da ya gudana jiya Talata a birnin Abuja na Najeriya, Babban hafsan sojin Najeriya Janar Abayomi Gabriel Olonisakin ya ce daga Lokacin da aka kafa Rundunar hadin gwiwa na kasashen yankin tabkin Tchadi (MNJTF),Shakka babu hare-haren da kungiyar boko haram ke kaiwa ya ragu sosai, sannan ya kara da cewa ya kamata a kara samun hadin kai a tsakanin Sojoji domin kawar da kungiyar boko haram gaba daya a yankin.

A nasa bangare babban komandan Rundunar hadin gwiwa na yankin Tabkin tchadi  Manjo-janar Lamidi Adeosun ya ce duk da cewa an karya lagon mayakan kungiyar boko haram din a wasu yankuna to amma har yanzu akwai sauran rina a kafa don kuwa har yanzu suna ci gaba da kai hare-haren harin sari ka noke a wasu yankunan kasashen domin haka wajibi ne Sojojin su kara dagewa domin tabbatar da tsaro a yankin.

Rundunar hadin gwiwa na kasashen yankin tabkin Tchadi ta hada da Sojojin kasashen niger, nigeria, Kamaru da Tchadi.