An sace wasu 'yan kasar Jamus a jihar Kaduna
Feb 23, 2017 10:54 UTC
Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tura jami'an 'yan sanda na musaman bayan samun rahoton sace wasu yan kasar Jamus guda biyu a kauyen Jajela dake Jihar Kaduna.
Kakakin Hukumar ‘yan sandan Nigeria Aliyu Usman ya ce mutanen kauyen ne suka shaida musu sace mutanen biyu wadanda suka je aiki ba tare da jami’an tsaron dake kare lafiyar su ba. ana kyautata zaton cewar masu satar mutane dan karbar kudin fansa ne suka sace su
Jamusawan masu bincike ne na abubuwan tarihi da ke karkashin kasa, wadanda suka ziyarci kauyen Jajela da ke karamar hukumar Kagarko a jihar Kaduna.
A halin da ake ciki, babu wani mutum da ya tuntubi 'yan uwan Jamusawan ko Gwamnati domin sakin Jamusawan,
Tags