Mali : Matasa Sun Farmawa Wuraren Saye Da Shan Barasa A Tunbuctu
Matasa a birnin Tumbuctu dake arewacin kasar Mali sun farmawa wuraren saye da sayarwa da kuma shan barasa, wanda suka danganta da wuraren bata tarbiya.
Wani mazaunin daya ganewa idonsa lamarin ya shaidawa kanfanin dilancin labaren AFP matasan sun wargaza wuraren tare da farfasa kwalabe da duk wata irin barasa a wuraren da suka hada da zuraren shakatawa, gidaje da shaguda da dai saurensu.
Ba'a dai samu labarin hasaran rai ba ko kuma raunana a lamarin ba kamar yadda wata majiyar 'yan sanda ta shaidawa kanfanin dilancion labaren AFP.
Daya daga cikin matasan da suka shirya boren ya shaida cewa sunyi la'akari da cewa wuraren saida barasa da kuma sha na dada karuwa a yankin don haka ba zasu lamunta da hakan ba a kasa ta musulunci.
Bayanai daga yankin sun har matasan suka gama borensu da kuma fashe fashe basu fuskanci wata turjiya ba daga jami'an tsaro.