An Yi Garambawul A Sabuwar Majalisar Ministocin Kasar Tunisia
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18040-an_yi_garambawul_a_sabuwar_majalisar_ministocin_kasar_tunisia
Majalisar ministocin kasar Tunisia da aka kafa watanni biyar da suka gabata, ta gudanar da wasu canje-canje a wasu daga cikin ma'akatun kasar da suka shafi ministocin wadannan ma'aikatu.
(last modified 2018-08-22T11:29:44+00:00 )
Feb 26, 2017 12:15 UTC
  • An Yi Garambawul A Sabuwar Majalisar Ministocin Kasar Tunisia

Majalisar ministocin kasar Tunisia da aka kafa watanni biyar da suka gabata, ta gudanar da wasu canje-canje a wasu daga cikin ma'akatun kasar da suka shafi ministocin wadannan ma'aikatu.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, Yusuf Shahid firayi ministan kasar Tunisia, ya sanar da sauye-sauyen ne a daidai lokacin da kasar take kokarin ganin cewa sabuwar gwamnatin hadin kan kasa da aka ta samu nasara a cikin ayyukanta.

Ma'aikatun da sauye-sauyen suka shaf akuwa sun hada da ma'aikatar ayyuka da kuma maiakkatar da ke kula da harkokin addini ta kasar.