Jami'an Tsaron Senegal Sun Damke Wasu Da Ake Zargi Da Ayykan Ta'addanci
(last modified Sun, 26 Feb 2017 12:16:23 GMT )
Feb 26, 2017 12:16 UTC
  • Jami'an Tsaron Senegal Sun Damke Wasu Da Ake Zargi Da Ayykan Ta'addanci

Jami'an tsaron kasar Senegal sun damke wasu mutane biyu dukkanin 'yan kasar Mali da ake zargin suna da hannu a hare-haren ta'addancin a kasar Ivory Coast a cikin watan Mris 2016.

Shafin yada labarai na Afirka Time ya bayar da rahoton cewa, kakakin rundunar 'yan sanda a kasar Senegal Henry Boumy Ciss ya sheda cewa, an damke mutanen biyu biyu ne a jiya a birnin Dakar.

Henry Boumy Ciss ya kara da cewa, dukkanin mutanen biyu suna nan suna gudanar da bincike a kan lamarinsu.

Harin da aka kai a kan wani katafaren otel a kusa da birnin Abijana cibiyar kasuwanci a kasar Ivory Coast a 2016 ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 19 tare da jikkatar wasu fiye da 20.