Wasu kabilu sun bukaci ballewa daga kasar Aljeriya
Wata sabuwar kungiyar kabilu a yankin gabashin kasar Aljeriya ta bayyana kanta tare da aniyar kafa Gwamnati mai cin kashin kai a kasar
Kamfanin dillancin Labaran Jamus ya habarta a ranar Juma'ar da ta gabata, wasu kabilu sun gudanar da wani taro da suka bashi Lakabin Tajamu'u min ajali Kaba'il a kauyen Arus dake karamar gundumar Ayatu Umalu na jihar Tizi wazu inda suka rattaba hanu a kan hada kai wajen neman samun kasa mai cin gashin kanta.
Hamu Bu madin mai tuntubar juna a tsakanin Kabilun ya bayyana cewa taron Attajamu'u min Ajali Kaba'il na bukatar Gwamnatin Aljeriya da ta amince da yankin Kabilun kasar kuma ta basu izinin samar da cibiyoyi gami da kafa Gwamnati da kuma samar da Majalisa mai cin gashin kanta.
Wannan sabon hadin kan kabilun na zuwa ne a yayin da Gwamnatin kasar Aljeriya ke fuskantar barazanar tsaro na 'yan ta'adda, inda a kwanakin baya bayan nan Dakarun tsaron kasar suka fadada kai hare haren su a kan kungiyoyin 'yan ta'adda a yankuna daban daban na kasar