Aljeriya : Dan Kunar Bakin Wake Ya Raunata 'Yan Sanda 3
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18066-aljeriya_dan_kunar_bakin_wake_ya_raunata_'yan_sanda_3
Rahotanni daga Aljeriya na cewa, wasu 'yan sanda uku sun jikkata lokacin da wani dan kunar baki wake ya tarwatsa kansa a kusa da wani ofishin 'yan sanda dake garin Bab el Kantara a gabashin lardin Constantine.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Feb 27, 2017 02:13 UTC
  • Aljeriya : Dan Kunar Bakin Wake Ya Raunata 'Yan Sanda 3

Rahotanni daga Aljeriya na cewa, wasu 'yan sanda uku sun jikkata lokacin da wani dan kunar baki wake ya tarwatsa kansa a kusa da wani ofishin 'yan sanda dake garin Bab el Kantara a gabashin lardin Constantine.

Bayanai sun nuna cewa wani dan sanda ne ya budewa dan kunar bakin waken wuta a lokacin da yake kokarin tayar da bam din dake jikinsa a wajen ofishin 'yan sanda.

Bayan dan kunar bakin waken ya fadi kasa ne kuma sai nan da nan ya tayar da bam din da ke makale a jikinsa, inda ya kashe kansa kana ya jikkata wasu jami'an 'yan sanda uku.

Kasar Aljeriya dai tana ci gaba da fuskantar barazanar ta'adddanci, sakamakon matsalar tsaro da rigingimun siyasa da yankin ke fuskanta. 

ko ranar 28 ga watan Nuwamba bara wasu 'yan bindiga da ake kautata zaton mayakan islama ne sun kashe wani babban jami'in 'yan sanda a wani gidan cin abunci.

A makon daya gabata rundinar sojin kasat ta Aljeriya ta sanar da hallaka wasu mayakan islama 14 a wani babban samame data kai a yankin Buyira dake kudancin Aljas babban birnin kasar.