Shugaba Umar Al-bashir na Sudan ya nada Firaminista
(last modified Thu, 02 Mar 2017 05:09:22 GMT )
Mar 02, 2017 05:09 UTC
  • Shugaba Umar Al-bashir na Sudan ya nada Firaminista

A daren jiya Laraba Shugaban Kasar Sudan Umar Al-bashir ya nada Bakari Hasan Salah a matsayin sabon Firaministan kasar.

Tun daga lokacin da Shugaba Albashir ya dare kan karagar milkin kasar Sudan, Bakari Hasan Salah shi ne farko wanda ya riki mikamin Minista a kasar ta Sudan, a shekarar 1989 ya kasance gungu a cikin Majalisar juyin juya halin kasar, daga  shekarar 1990, Mista Bakari ya rike mikamin wakilin Shugaban kasa a hukumar tsaron kasar kuma Shugaban kwamitin, daga shekarar 1995 zuwa 1998 Ministan cikin gida, sannan kuma a shekarar 2005 ya zama Ministan tsaron kasar kuma Minista a fadar Shugaban kasa har zuwa shekarar 2013, bayan ga hakan daga shekarar 2013 zuwa daren jiya Laraba Mista Bakari Hasan Salah na kire ne da matsayin Mataimakin Shugaban kasar.

A baya-bayan ne dai Majalisar dokokin kasar ta kada kuri'a da gagarimar rinjaye na gudanar canje-canje a kundin tsarin milkin kasar tare kuma da samar da matsayi na Firaminista a kasar. wanda dai shi ne karo na farko da aka gudanar da canji a kundin tsarin milkin kasar Sudan din tun bayan da Shugaba Albashir ya dare kan karagar milki a shekarar 1993.