'Yan Sandan Kongo Sun Kame Shugaban Wata Kungiyar Asiri Ta Kasar
(last modified Sat, 04 Mar 2017 05:53:10 GMT )
Mar 04, 2017 05:53 UTC
  • 'Yan Sandan Kongo Sun Kame Shugaban Wata Kungiyar Asiri Ta Kasar

'Yan sandan kasar Demokradiyyar Kongo sun ce sun sami nasarar kame shugaban wata kungiyar Kiristoci ta asiri a babban birnin kasar, Kinshasa bayan rikici na kimanin makonni biyu da yayi sanadiyyar mutuwar mutane shida daga cikin magoya bayansa.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya bayyana cewar 'yan sandan sun bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da suka fitar dauke da sanya hannun kakakin 'yan sandan Pierre Mwanamputu inda suka ce jami'an tsaron kasar sun sami nasarar kama Ne Muanda Nsemi, wanda memba ne a majalisar kasar kana kuma shugaban kungiyar Bundu dia Kongo (BDK) ta asiri din tare da matarsa.

Sanarwar 'yan sandan dai ba ta yi karin bayani kan yadda aka yi aka kama shi shugaban wannan kungiyar ba da kuma wadanda suka rasa rayukansu, sai dai kuma kamfanin dillancin labaran Reuters din ya ce wasu shaidun gani da ido sun shaida masa cewa 'yan sandan sun bindige wasu magoya bayan wannan kungiyar su biyu a jiyan kafin suka kama shugaban nasu.

Shi dai Mr. Nsemi, wanda yake kiran kansa a matsayin Annabi, yana da magoya baya masu yawa lardin Central Congo da ke Kudu maso yammacin kasar wanda kuma suke kokarin sake raya tsohuwar masarautar Kongo mai dadadden tarihi.