Cutar korala ta hallaka Mutane da dama a kasar Somaliya
Firaministan kasar Somaliya ya sanar da billar wata annoba da ta yi sanadiyar mutane da dama a kasar
A cikin wani jawabi da ya gabatar a wannan Assabar Firaministan kasar Somaliya Hasan Ali Khaira ya sanar da billar annoba a yankin Bay dake kudu maso yammacin kasar, inda tuni ta kashe 'yan kasar akalla 110 yayin da wasu da dama ke cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.
Firaministan ya ce shakka babu asarar rayukan da aka samu ya biyo bayan karamcin ruwa ne da kuma tsananin farin da kasar ta fuskanta domin haka sabuwar Gwamnati ta kudiri magance wannan matsala cikin gaggawa.
A bangare guda, Muhamad Hasan Faiki daya daga cikin shugabanin jihar kudu maso yammacin kasar ya bayyana cewa Mutanan da suka kamu da wannan cuta na cikin mayuwacin hali ta yadda jami'an kiyon lafiya na Jihar ba za su iya basu kulawa ba kamar yadda ya kamata domin haka ana bukatar taimakon gaggauwa daga kungiyoyin kasa da kasa.
A nata bangare Hukumar Lafiya ta Duniya ta sanar da cewa dole ne a dauki matakan gaggauwa na dakile wannan annoba domin haka tuni ta tura Jami'anta gami da taimakon magani zuwa kasar ta Somaliya.