Tawagar Kwamitin Tsaron MDD Ta Isa Jahar Borno Ta Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18258-tawagar_kwamitin_tsaron_mdd_ta_isa_jahar_borno_ta_najeriya
Tawagar kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ta isa birnin Maiduguri na jahar da ke arewa maso gabashin najeriya a yau, domin duba halin da ake ciki kan matsalolin da ake fuskanta sakamakon ayyukan kungiyar Boko Haram.
(last modified 2018-08-22T06:59:46+00:00 )
Mar 05, 2017 14:06 UTC
  • Tawagar Kwamitin Tsaron MDD Ta Isa Jahar Borno Ta Najeriya

Tawagar kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya ta isa birnin Maiduguri na jahar da ke arewa maso gabashin najeriya a yau, domin duba halin da ake ciki kan matsalolin da ake fuskanta sakamakon ayyukan kungiyar Boko Haram.

Tawagar wadda ta kunshi wakilan dukkanin mambobin kwamitin tsaro 15 ta isa Najeriya ne bayan kammala ziyarar aiki a jamhuriyar Nijar, inda ta gana mahukuntan kan matsalolin da rikicin Boko Haram ya jawo a kasar musamman ta fuskar tsaro, kafin na kuma ta ziyarci Chadi da Kamaru, wadanda dukkaninsu suna cikin kasashen yankin tafkin Chadi.

Tawagar dai za ta gana da mahukunta na jahar Borno, da kuma wasu daga cikin magaddan gari a yankunan da rikicin Boko haram yafi shafa a cikin jahar, kamar yadda kuma za su duba wasu sansanonin 'yan gudun hijira domin gane wa idanunsu halin da suke ciki, a gobe Litinin kuma za su isa Abuja domin ganawa da jami'an gwamnatin tarayyar Najeriya.