Hadewar kungiyoyin masu tsaurin ra'ayin addini wuri guda a kasar Mali
Wani sabon hadin gwiwa tsakanin kungiyoyin Ansarudin da Almrabitun da Duniya ke kalonsu a matsayin kungiyoyin 'yan ta'adda a kasar Mali
Wannan sabuwar kungiya ta Hadin gwiwa mai sunan Jama'atu Nusratul-Islam wal musulimin za ta kasance kalkashin Jagorancin Iyad Ag Ghali Shugaban kungiyar Ansarudin, wadannan kungiyoyin masu tsaurin ra'ayi da Duniya ke yi wa kallon kungiyoyin 'yan ta'adda ya zuwa yanzu sun dauki alhakin hare-haren da aka kaiwa Dakarun tsaron Mali, da Dakarun wanzar da zaman Lafiya na MDD gami da Dakarun kasar Faransa dake gudanar da aiyukan tabbatar da tsaro a kasar ta Mali.
Kungiyar Almurabitun wacce ke da alakar kut da kut da kungiyar Alka'ida dake kalkashin jagorancin Mukhtar bn Mukhtar Aljazaery ta dauki alhakin harin Bam din da aka kai sansanin Sojin Mali dake birnin Gao na arewacin kasar, harin da ya yi sanadiyar mutuwar Mutane 60 da kuma jikkatar wasu sama da 100 na daban.
Ko baya da wannan, an bayyana cewa Kungiyoyin Garden Masina dake gudanar da aiyukanta a tsakiyar kasar ta Mali gami da Kungiyar Imaratu Sahara nan ba da jimawa ba za su hade da wannan sabuwar hadin gwiwa na kungiyar Jama'atu Nusratul-Islam wal musulimin. wannan hadin kai na kungiyoyin masu tsatsaurin ra'ayi na zuwa ne a yayin da Gwamnatin ta Mali ke shirin zartar da yarjejjeniyar Sulhun da suka cimma tsakanin su da kungiyoyin 'yan tawaye na arewacin kasar domin kawo karshen tashin hankali da rashin tsaro da kasar ke fuskanta.
Duk da cewa kasar ta Mali ta kwashe tsahon shekaru tana fama da rikice rikicen Siyasa da na 'yan tawaye gami da na 'yan ta'adda to amma wannan hadin kai na kungiyoyin 'yan ta'adda ya tilastawa Gwamnatin ta Mali zartar da yarjejjeniyar Sulhu da suka cimma a shekarar 2015 tare da kungiyoyin 'yan tawaye na arewacin kasar. wannan mataki da Gwamnatin ta Mali ta dauka zai taimaka wajen tunkarar 'yan ta'addar da suka hada kai domin yakar Gwamnatin.
Tun a ranar 2 ga wannan wata na Maris da muke ciki ne aka zartar da wannan yarjejjeniya, bayan da aka nada Shugani a yankunan Kidal, Gao, Tounbouctou da Manaka,an zabi wadannan Shugabanin ne a tsakanin wakilan Kungiyoyin 'yan tawayen arewacin kasar da kuma na Gwamnati.baya ga haka an kafa wada rundunar hadin gwiwa tsakanin 'yan tawayen arewacin kasar da na Gwamnati da su dinga sintiri a cikin yankunan saharar kasar. masana harakokin tsaro na ganin cewa wannan mataki da Gwamnatin ta Mali ta dauka zai taimaka wajen rage karfi da kuma hare-haren da kungiyoyin 'yan ta'adda ke kaiwa kan jami'an tsaron kasar.inda wasu ma ke ganin cewa wannan hadin gwiwa na Gwamnatin ta Mali da bangaren 'yan tawaye shi ne ya sanya kungiyoyin 'yan ta'adda suma suka hade wuri guda domin hade karfinsu na yadda za su tunkari Gwamnatin ta Mali.
A cikin 'yan kwanakin nan dai kungiyoyin 'yan ta'addar dake cikin kasar Mali sun tasananta kai hare-haren su kan Dakarun kasar inda ko a ranar Lahadin da ta gabata sai da suka kaiwa Sojoji hari tare da kashe 10 daga cikin su, baya ga kasar ta Mali 'yan ta'adda sun kai hari ga Sojojin kasar Nijer a kan iyakar kasar da Mali tare da kashe akalla 15 daga cikin su sannan kuma sun kai irin wannan hari na ta'addanci a wani kauye dake cikin kasar Burkina Faso tare da kashe wani malamin makaranta da dalibai guda biyu.