An Kashe Sojojin Mali 11 A Iyaka Kasar Da Burkina Faso
Ma'aikatar tsaro a Mali ta sanar da mutuwar wasu sojojin kasar 11 da kuma wasu 5 da suka raunana a yayin wani hari da aka kai masu a yankin Boulkessi dake kan iyaka da Burkina Faso.
Sanarwar da aka karanto a gidan talabijin din kasar ta ce an kaiwa sojojin hari ne da sanyin safiyar jiya Lahadi, a barikinsu dake Boulkessi a tsakiyar kasar a iyaka da Burkina Faso.
Wasu bayanai na daban sun ce maharan sun kuma kwashi makamai masu yawa kafin su bamkawa sauren makaman wuta.
Har kawo yanzu babu wata kungiya da ta dau alhakin kai harin, saidai fa tuni aka fara nuna 'yar yasa ga kungiyar nan mai kaifin kishin islama ta (Ansarul Islam) data yi kaurin suna wajen aikata ire-iren wadannan ayyukan ta'adi a yankin.
A baya bayan nan dai hare haren ta'adanci na dada karuwa a tsakiyar kasar ta Mali, wanda a cen baya aka saba ganinsu a arewacin kasar.