Aljeriya Ta Kara Daukar Tsaurarar Matakai A Kan Iyakokinta
Babban hafsan hafsoshin sojin kasar Aljeriya Janar Ahmad Kai'd Saleh ya sanar da cewa, kasarsa ta fara daukar tsauraran matakai a kan iyakokinta, domin fuskantar barazanar da 'yan ta'adda ke yi wa kasar daga kasashen da ke makwaftaka da ita.
Tashar talabijin ta Russia Today ta bayar da rahoton cewa, a zaman da babban kafsan hafsoshin sojin kasar ta Aljeriya janar Ahmad Kaid Saleh ya gudanar a jiya tare da sauran hafsoshi da manyan jami'an tsaron kasar, ya tabbatar musu da cewa, sabon shirin tsaron iyakokin kasar ya fara aiki, musamman a kan iyakokin kasar da kasashen Libya da Mali.
Daga farkon wannan shekara ta 2017, jami'an tsaron kasar Aljeriya sun kashe 'yan ta'adda fiye da 130 a kan iyakokin kasar da kasashen Mali da Libya, tare da kame wasu 225, tare da kame tarin makamai da suka hada da daruruwan bindigogi, da kuma makaman roka.