Taron Gamayyar Kungiyoyin Matasa Musulmi A Senegal
(last modified Tue, 07 Mar 2017 08:10:25 GMT )
Mar 07, 2017 08:10 UTC
  • Taron Gamayyar Kungiyoyin Matasa Musulmi A Senegal

An gudanar da taron gamayyar kungiyoyin matasa musulmi na shekara-shekara a kasar Senegal.

Kamfanin dillancin labaran Mehr ya bayar da rahoton cewa, an gudanar da babban taron gamayyar kungiyoyin matasa musulmi na kasar Senegal a birnin Dakar fadar mulkin kasar, mai take sulhu da zaman lafiya.

Wannan taro dai ana gudanar da shi a karo na hudu kenan a kasar ta Senegal, a wannan karon karon taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnati da kuma manyan malamai da ma wasu jami’an diflomasiyya na kasashen musulmi.

Karamin jakadan kasar Iran a kasar Senegal Sayyid Hassan Esmati ya gabatar da jawabi a wurin taron, inda ya bayyana cewa har kullum matasa su ne kashin bayan kowace al’umma, domin kuwa a kansu ne ake gina duk wani buri da kowace al’umma za ta zama a gaba.

Ya ce ko shakka babu, kasar Senegak na daga cikin kasashen musulmi a nahiyar Afirka ta yamma da suke bayar da himma wajen ganin sun kula da matasa, inda malaman addini musamman musamman malaman makarantun darikoki na sufaye suke taka gagarumar rawa wajen tarbiyantar da matasa a kan tafarkin addini da tsarkake ruhi da bautar Allah.

Wasu daga cikin manyan malaman darikun Tijjaniya da muridiyya sun halrci wurin, kamar yadda kuma wasu ‘yan kasashen ketare musamman daga kasashen larabawa da ma wasu kasashen Afirka da suke zaune a Senegal sun halarci taron.