Sojojin Aljeriya Suna Ci Gaba Da Gudanar Da Samame A Yankunan Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18316-sojojin_aljeriya_suna_ci_gaba_da_gudanar_da_samame_a_yankunan_kasar
A ci gaba da samame da sojojin gwamnatin Aljeriya ke gudanarwa a yankuna daban daban na kasar da nufin murkushe ayyukan ta'addanci, sojojin sun samu nasarar kashe 'yan ta'adda biyu a yankin arewacin kasar.
(last modified 2018-08-22T11:29:47+00:00 )
Mar 07, 2017 18:20 UTC
  • Sojojin Aljeriya Suna Ci Gaba Da Gudanar Da Samame A Yankunan Kasar

A ci gaba da samame da sojojin gwamnatin Aljeriya ke gudanarwa a yankuna daban daban na kasar da nufin murkushe ayyukan ta'addanci, sojojin sun samu nasarar kashe 'yan ta'adda biyu a yankin arewacin kasar.

Ma'aikatar tsaron kasar Aljeriya ta fitar da bayanin cewa: Sojojin gwamnatin kasar a safiyar yau Talata sun kaddamar da wani hari kan wata maboyar 'yan ta'adda da ke lardin Boumarados a shiyar arewacin kasar, inda suka yi nasarar halaka 'yan ta'adda biyu tare da cafke wasu biyu na daban.

Bayanin ya kara da cewa: Sojojin gwamnatin kasar sun yi nasarar gano tarin makamai a maboyar 'yan ta'addan tare da tattara su a matsayin ganima. A halin yanzu haka dai sojojin gwamnatin Aljeriya sun tsananta gudanar da samame a sassa daban daban na kasar na nufin kawo karshen ayyukan ta'addanci a kasar musamman a yankunan da suke kusa da kan iyaka da kasashen makobtanta.