Mali: Fararen Hula Suna Fuskantar Matsalar Tabarbarewar Harkokin Tsaro
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18392-mali_fararen_hula_suna_fuskantar_matsalar_tabarbarewar_harkokin_tsaro
Majalisar Dinkin Duniya ta ce Mazauna arewacin kasar Kasar Mali Suna furkantar matsalolin rashin tsaro da koma bayan tattalin arziki
(last modified 2018-08-22T06:59:47+00:00 )
Mar 10, 2017 09:12 UTC
  • Mali:  Fararen Hula Suna Fuskantar Matsalar Tabarbarewar Harkokin Tsaro

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Mazauna arewacin kasar Kasar Mali Suna furkantar matsalolin rashin tsaro da koma bayan tattalin arziki

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Mazauna arewacin kasar Kasar Mali Suna furkantar matsalolin rashin tsaro da koma bayan tattalin arziki.

 A wani bayani da Majalisar Dinkin Duniyar ta fitar ta bakin wani kwararrenta a fagen kare hakkin bil'adama Suliman Baldo, wanda ya ke ziyarar aiki a kasar Mali, ya ce; Fararen hula a arewacin kasar ta Mali suna fuskantar hatsari mai girma saboda hare-haren da masu adawa da gwamnati su ke kai wa.

Bayanin ya ci gaba da cewa; Tare da cewa da akwai sojojin gwamnati da aka girke a yankin da su ka kafa wuraren bincike na kan iyaka, sai dai duk da haka masu adawa da gwamnati suna ci gaba da kai hare-hare, haka nan kuma 'yan fashi.

Sulaiman Baldo ya kuma bukaci kungiyoyin kasa-kasa da su kara azama wajen taimakawa kasar ta Mali domin aiwatar da yarjejeniyar sulhu ta 2015.