Goyon bayan Duniya na warware rikicin siyasar kasar Siriya ta hanyar Siyasa
Ministan harakokin wajen Masar ya bayyana cewa Duniya ta dowa daga tunanin warware rikicin kasar Siriya ta hanyan amfani da karfi.
Yayin da yake magana da Jaridar Alwatan ta kasar, Ministan harakokin wajen Masar Samih Shukri ya bayyana cewa Kungiyoyin Duniya da kuma kasashen Larabawa sun dawo da tunanin warware rikicin kasar Siriya ta hanyar amfani da karfin Soja, dukkanin tunaninsu ya koma kan yadda za a magance rikicin ta hanyar Siyasa.
Shukri ya kara da cewa dukkanin kasashen Duniya sun fahimci cewa babu yadda za a magance rikcin kasar ta Siriya ta hanyar amfani da karfi domin haka, ko wata kasa na kokarin bada gudumuwarta na ganin an warware rikicin ta hanyar siyasa.yayin da yake ishara kan matsayin kasar Siriya a kungiyar hadin kan kasashen Larabawa, Ministan harakokin wajen Masar din ya ce kasar Siriya kasa ce ta Larabawa kuma za ta ci gaba da zama rukuni na tsarin kasashen Larabawa, dangane da komawarta kuma cikin kungiyar ya ce daga karshe dole ne hakan ya kasance a aikace.
Daga karshe Ministan ya ce kamata ya yi kasar ta ci gaba da kokari wajen samar da wani sabon tsari da zai samu amincewar Al'ummar kasar baki daya.