Gwamnatin Mali Da 'Yan Tawaye Suna Ci Gaba Da Tattaunawa
Mar 11, 2017 03:14 UTC
Bangarorin gwamnatin Mali da kuma 'yan tawayen arewacin kasar na ci gaba da gudanar da tattaunawa da nufin samun sulhu mai dorewa.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a jiya an gudanar da zama a tsakanin bangarorin gwamnati da kuma 'yan tawayen da ke iko da birnin Tinbuktu da ke arewacin kasar.
Babbar kungiyar 'yan tawayen wadda ta kunshi abzinawa da kuma larabawa da iko da birnin Tinbukto, ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya tare da bangaren gwamnatin Mali, kan mika iko da muhimman wurare da suke rike da su a cikin birnin, tare da janye shingayen bincike da suka kafa a kan tituna.
Tags