Wasu 'Yan Ta'adda Sun Kai Hari Kan Dakarun Tsaron Kasar Tunusiya
Wasu gungun 'yan ta'adda sun kaddamar da hari kan tawagar jami'an tsaron Tunusiya a yankin kudancin kasar.
Gidan talabijin na Sky News ya watsa rahoton cewa: Wasu gungun 'yan ta'adda sun kaddamar da harin wuce gona da iri kan tawagar jami'an tsaron Tunusiya da suke gudanar da sintiri a lardin Qabli da ke kudancin kasar lamarin da ya haifar da musayar wuta tsakanin bangarorin biyu da ya janyo mutuwar soja guda da 'yan ta'adda biyu.
Har ila yau musayar wutan ta yi sanadiyyar jikkatan sojan gwamnatin Tunusiya guda, amma har ya zuwa yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.
Tun bayan kifar da gwamnatin kama karya ta Zainul-Abideen bin Ali a shekara ta 2011 a Tunusiya, kasar ta fara fuskantar tsoma bakin kasashen waje tare da kunna wutan ta'addanci a kasar.