MDD: Yunwa Na Barazana Ga Al'ummomin Arewacin Kasar Kenya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18594-mdd_yunwa_na_barazana_ga_al'ummomin_arewacin_kasar_kenya
Majalisar dinkin dinkin duniya ta yi gargadin cewa, yunwa za ta halaka mutane masu yawa a arwacin Kenya matukar dai ba a kai musu daukin gaggawa ba.
(last modified 2018-08-22T11:29:49+00:00 )
Mar 17, 2017 17:17 UTC
  • MDD: Yunwa Na Barazana Ga Al'ummomin Arewacin Kasar Kenya

Majalisar dinkin dinkin duniya ta yi gargadin cewa, yunwa za ta halaka mutane masu yawa a arwacin Kenya matukar dai ba a kai musu daukin gaggawa ba.

Shafin yada labarai na World Bulletin ya bayar da rahoton cewa, babban jami'in majalisar dinkin duniya  akasar Kenya Siddharth Chatterjee ya bayyana cewa, sakamakon matsalar karancin ruwan sama da aka samua  yankunan arewacin kasar Kenya, al'ummar wadannan yankuna na cikin matslar karancin abinci.

Ya ce akwai kimanin mutane miliyan 3 a halin yanzu da suka bukatar agajin abinci cikin gaggawa  a cikin yankuna 23 daga cikin yankuna 47 da wanann matsala ta shafa a rewacin kasar Kenya.