'Yan Bindiga Sun Kashe Kakakin Rundunar 'Yan Sandan Kasar Uganda
Wasu masu dauke da makamai sun kashe kakakin rundunar 'yan sandan kasar Uganda a yau a birnin kampala tare da wasu jami'an 'yan sanda biyu.
Kamfanin dillancin labaran IRIB ya bayar da rahoton cewa, babban sufeton 'yan sanda na kasar Uganda Kale Kayihura ya fadi a yau cewa, wasu masu dauke da makamai sun kai wa kakakin rundunar 'yan sanda ta kasar Andrew Kaweesi hari da safiyar yau Juma'a, a lokacin da yake fitowa daga gidansa da ke yankin Kulambiro a cikin birnin Kampala.
Babban sufetun 'yan sandan na kasar Uganda ya kara da cewa, 'yan bindigar sun kasashe Andrew Kaweesi ne tare da wasu jami'an 'yan sanda biyu da suke tare da shi, a lokacin da yake shirin tafiya ofishinsa.
Ya ce babu wata kungiya ko gungun wata jama'a da ya suka dauki alhakin kai wannan hari, amma tuni an shiga gudanar da bincike kan lamarin.