Mali : An kashe Kwamandan Mayakan Dake Goyan Bayan Gwamnati
Rahotanni daga Mali na cewa an kashe kwamadan kungiyar 'yan tawayen (GATIA) mai goyan bayan gwamnatin kasar.
An dai kashe Almahdi Ag Iengach ne a yankin Menaka dake arewa maso gabashin kasar a jiya Juma'a, kuma har kawo yanzu babu karin bayyani akan kisan na sa.
Kisan na Ag Iengach na zuwa ne a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar tsaro da kuma kasa kafa hukumomin wucin gadi a yankunan Tombouctou da Taoudeni.
har kawo yanzu dai gwamnatin kasar bata ce uffan ba, saidai tuni wasu majiyoyi a yankin suka shaidawa kanfanin dilancin labaren AFP cewa labarin bai rasa nasaba da daukan fansa.
Shi dai Ag Iengach na jagorantar kungiyar ta GATIA ne a wannan yankin da mayakan dake goyan bayan gwamnati, da tsaffin 'yan tawaye CMA da kuma dakarun gwamnatin sojin ta Mali ke yaki da mayakan dake ikirari da sunan jihadi.