Kasashen Tunusiya Da Sudan Sun Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Taimakekkeniya
Gwamnatocin kasashen Tunusiya da Sudan sun dauki matakin kara bunkasa alaka da taimakekkeniya a tsakaninsu ta hanyar rattaba hannu kan yarjeniyoyi har 22.
Kamfanin dillancin labaran China na Shin Huwa ya watsa rahoton cewa: A karshen zaman tattaunawa a tsakanin fira ministan Tunusiya Yusuf Shahid da takwararsa na Sudan Bakri Hassan Saleh jami'an kasashen biyu sun rattaba hannu kan tarin yarjeniyoyi har 22 da nufin bunkasa alaka da taimakekkeniya a tsakanin kasashensu musamman a bangarorin da suka shafi kiwon lafiya, yawon shakatawa, ilimi, musayar fasaha, gona da sauransu.
Har ila yau a bayan gudanar da zaman tattaunawan fira ministan kasar Tunusiya Yusuf Shahid ya bayyanawa manema labarai cewa: Daga nan zuwa watan Satumban wannan shekara ta 2017 za a fara samun safarar jirage kai tsaye a tsakanin kasashen Tunusiya da Sudan.
Tun a ranar Laraba da ta gabata ce fira ministan kasar Tunusiya Yusuf Shahid ya fara gudanar da ziyarar aiki na kwanaki biyu a kasar ta Sudan.