Bukatar MDD na tsagaita wuta cikin gaggawa a Sudan ta Kudu.
(last modified Fri, 24 Mar 2017 11:02:31 GMT )
Mar 24, 2017 11:02 UTC
  • Bukatar MDD na tsagaita wuta cikin gaggawa a Sudan ta Kudu.

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci bangarorin dake fada da juna a kasar Sudun ta kudu da su kawo karshen fada tare zartar da yarjejjeniyar tsagaita wuta.

A cikin wata sanarwa da Kwamitin tsaron MDD wacce Ministan harakokin wajen Italiya ya karanta a jiya Alkhamis, ta bukaci bangarorin dake fada da juna a kasar Sudun ta kudu da su kawo karshen fada tare zartar da yarjejjeniyar tsagaita wuta cikin gaggawa.

A yayin da suke bayyana damuwar su kan halin da Al'ummar Sudan ta kudu ke ciki, Mambobin Kwamitin sun ce daukan matakin soja ba zai kawo karshen rikicin kasar ba, inda suka bukaci bangarorin dake fada da juna da su rungumi yarjejjeniyar sulhu da suka cimma a tsakanin su bisa shiga tsakani na Majalisar Dinkin Duniya.

Tun a watan Decembar shekarar 2013, kasar Sudan ta kudu ta fada cikin rikici bayan da Shugaba Salva keir ya sauke mataimakinsa Riek Machar, a watan Augustan 2015, bangarorin biyu sun cimma yarjejjeniyar tsagaita wuta, sai dai tun kafin aje ko ina , yarjejjeinyar ta rushe.