Alkalai Sun Sake Tsunduma Cikin Yajin Aiki A Kasar Tunusiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18898-alkalai_sun_sake_tsunduma_cikin_yajin_aiki_a_kasar_tunusiya
Alkalai sun sake shiga cikin wani sabon yajin aiki a kasar Tunusiya suna neman gwamnatin kasar da ta gudanar da gyare-gyare a ma'aikatar shari'ar kasar da nufin kyautata rayuwarsu.
(last modified 2018-08-22T11:29:52+00:00 )
Mar 28, 2017 05:40 UTC
  • Alkalai Sun Sake Tsunduma Cikin Yajin Aiki A Kasar Tunusiya

Alkalai sun sake shiga cikin wani sabon yajin aiki a kasar Tunusiya suna neman gwamnatin kasar da ta gudanar da gyare-gyare a ma'aikatar shari'ar kasar da nufin kyautata rayuwarsu.

Alkalai a Tunusiya sun sake shiga wani sabon yajin aiki a duk fadin kasar daga jiya Litinin zuwa tsawon kwanaki uku domin jaddada bukatarsu ga mahukuntan kasar kan aiwatar da gyare-gyare a harkar tafiyar da ma'aikatar shari'ar kasar da nufin kyautata musu rayuwa, amma yajin aikin bai shafi bangaren kotunan da suke kula da harkokin kananan yara ko bada takardar izinin bisine gawawwaki ba.

Kungiyar Alkalai ta kasar Tunusiya ta sanar da cewa: Alkalan kasar suna fama da matsaloli masu yawa da suka hada da karancin albashi da rashin kwakkwaran matakan tsaro musamman ganin yadda ayyukan ta'addanci suke ci gaba da zama barazana ga rayukansu a kasar.

Wannan yajin aiki na alkalai a Tunusiya shi ne irinsa na biyu a kasa da wata guda, kuma karo na uku tun daga farkon wannan shekara ta 2017 da muke ciki, sakamakon yajin aikin da alkalan suka gudanar a ranar 27 ga watan Fabrairun daya gabata duk dai domin gwamnatin kasar ta share musu hawaye.