Red Cross: Lamurra Suna Kara Muni A Kasar Sakamakon Mummunan Fari
(last modified Wed, 29 Mar 2017 05:48:04 GMT )
Mar 29, 2017 05:48 UTC
  • Red Cross: Lamurra Suna Kara Muni A Kasar Sakamakon Mummunan Fari

Kungiyar bayar da agaji ta kasa da kasa Red Cross ta yi gargadi dangane da matsalar da ake fuskanta a wasu yankunan kasar Kenya sakamakon fari da aka fuskanta a kasar a daminar da ta gabata.

Tashar talabijin ta PressTV ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da kungiyar ta Red Cross ta fitar a jiya Talata, ta bayyana cewa a cikin watani uku da suka gabata ya zuwa yanzu, adadin mutanen da suke fama da matsalar yunwa a kasar Kenya ya rubanya har sau biyu, inda yanzu adadin ya kai mutane kimanin miliyan uku da suke bukatar agaji ta fuskar abinci.

bayanin ya ce hakan ta faru ne sakamakon matsalar karancin ruwan sama da aka samu a daminar da ta gabata a wasu yankuna na gabashin nahiyar Afirka, da hakan ya hada da Sudan ta kudu, Habasha da kuma kasar ta Kenya, akasarin wadanda matsalar tafi saurin shafa dai kananan yara ne.