Majalisar Dattawan Nijeriya Ta Dakatar Da Sanata Ali Ndume Na Watanni Shida
(last modified Wed, 29 Mar 2017 17:02:14 GMT )
Mar 29, 2017 17:02 UTC
  • Majalisar Dattawan Nijeriya Ta Dakatar Da Sanata Ali Ndume Na Watanni Shida

Majalisar dattawan Nijeriya ta dakatar da tsohon shugaban masu rinjaye na majalisar, Sanata Ali Ndume na tsawon watannni shida saboda bukatar da ya gabatar na a binciki shugaban majalisar Bukola Saraki da kuma Sanata Dino Melaye saboda aikata ba daidai ba.

A yau Laraba ce dai majalisar ta sanar da hakan bayan da kwamitin da'a na majalisar ya wanke shugaban majalisar Bukola Saraki daga zargin shigo da mota ba bisa ka'ida ba da kuma Sanata Dino Melaye daga zargin amfani da takardar shaidar digiri na bogi, zargin da Sanata Ali Ndumen ya bukaci majalisar da ta gudanar da bincike kansu.

A makon da ya gabata ne dai  Sanata Ndume ya nemi majalisar da ta gudanar da bincike kan labaran da kafar watsa labaran nan ta Sahara Repoters ta buga inda ta ce Sanata Saraki ya shigo da mota mai sulke Nijeriya ba bisa ka'ida, kamar yadda kuma ta zargi shi Sanata Dino Melaye da yin amfani da takardar digiri na bogi da ya ce ya samo su daga jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria.

An sami rarraubuwan kai tsakanin 'yan majalisar dangane da matakin da ya kamata a dauka kan Sanata Ndume din inda daga karshe dai majalisar da ta dakatar da shi na tsawon watanni shida maimakon shekara guda.

Wannan lamarin dai yana zuwa ne a daidai lokacin al'ummar Nijeriya suke ci gaba da nuna rashin jin dadinsu da yadda 'yan majalisar suke gudanar da ayyukansu musamman ci gaba da takun saka da suke yi da fadar shugaban kasa lamarin da ya sanya wasu kungiyoyi fara kiran da aka rusa majalisar.