Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu Ya Sauke Ministan Kudi Na Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18980-shugaban_kasar_afirka_ta_kudu_ya_sauke_ministan_kudi_na_kasar
Shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya sauke ministan kudi na kasar Parvin Gordhan daga kan mukaminsa.
(last modified 2018-08-22T11:29:53+00:00 )
Mar 31, 2017 06:36 UTC
  • Shugaban Kasar Afirka Ta Kudu Ya Sauke Ministan Kudi Na Kasar

Shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya sauke ministan kudi na kasar Parvin Gordhan daga kan mukaminsa.

Rahotanni daga kasar Afirka ta kudu sun ce fadar shugaban kasar ta sanar da cewa; shugaba Zuma ya sauke ministan kudin kasar Parvin Gordhan daga kan mukaminsa, kuma za a maye gurbinsa da Malusi Gigaba.

Tun kafin wannan lokacin dai an yi ta yada jita-jita a kasar a kan cewa; shugaba Zuma ya hana ministan kudin kasar fita daga kasar zuwa Amurka da kuma Birtaniya, babu wani karin bayani daga fadar shugaban kasa kan dalilin yin hakan, amma wasu na danganta hakan da zargin da fadar shugaba Zuma ke yi na aikata ba daidai ba a ma'aikatar kudi ta kasar.

Wasu daga cikin 'yan jam'iyyar ANC mai mulki da kuma jam'iyyar 'yan gurguzu da ke kawance da ita, sun nuna rashin amincewarsu da matakin da shugaba Jacob Zuma ya dauka na sauke Gordhan daga kan mukaminsa.