An Tsawaita Dokar Ta Baci A Mali
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19024-an_tsawaita_dokar_ta_baci_a_mali
Hukumomi a Mali sun tsawaita dokar ta bakin da aka kafa a kasar da kwanaki goma.
(last modified 2018-08-22T11:29:54+00:00 )
Apr 01, 2017 11:13 UTC
  • An Tsawaita Dokar Ta Baci A Mali

Hukumomi a Mali sun tsawaita dokar ta bakin da aka kafa a kasar da kwanaki goma.

Wannan matakin a cewar wata sanarwa hukumomin kasar na kara inganta al'amuran tsaro ne don yaki da ta'addanci da kuma karfafa aikin sa ido na sojojin kasar 

Tun watani 16 da suka wuce ne aka ayyana dokar ta baki a wannan kasa bayan harin ta'addanci da yayi sanadin mutuwar mutane 20 a watan Nuwamban 2015 a Otel din Radisson Blu dake Bamako babban birnin kasar.

A watan Yulin shekara 2016 data gabata an dai tsawaita dokar ne da watannin shida.

Kasar Mali kamar sauren makoftanta na yankin Sahel na fuskantar babbar barazana mayakan dake ikirari da sunan jihidi.