MDD Ta Tsawaita Aikin Tawagarta A RD Congo
Apr 02, 2017 06:52 UTC
MDD ta amunce da gagarimin rinjaye da tsawaita aikin tawagarta ta wanzar da zamen lafiya a Jamhuriya Demokuradiyyar Congo.
kudirin na MDD ya amunce da tsawaita aikin tawagar har zuwa 30 ga watan Satumba wannan shekarar.
An dai tafka muhawara mai zafi kafin amuncewa tsawaita aikin tawagar ta MONUSCO a cewar wakilin kasar faransa a MDD, Francois Delattre saboda barazanar sabuwar gwamnatin Donald Trump na Amurka na rage kasafin kudin da take bayarwa da kuma yawan sojojin.
Saidai kudirin ya tanadi rage yawan dakarun da kishi bakwai cikin dari, wanda daga addadin 19,000 da 'yan kai da ake da su a Congon, ya koma 16,000.
Tags