Gagarumar Zanga-Zangar A Gaban Majalisar Dattawan Nijeriya Kan Dakatar Da Ndume
(last modified Tue, 04 Apr 2017 16:48:00 GMT )
Apr 04, 2017 16:48 UTC
  • Gagarumar Zanga-Zangar A Gaban Majalisar Dattawan Nijeriya Kan Dakatar Da Ndume

Dubun dubatan masu zanga-zanga ne suka taru a gaban kofar shiga majalisar dokokin Nijeriya da ke birnin Abuja, babban birnin kasar suna masu bukatar da a janye dakatarwar da aka yi wa Sanata Ali Ndume wanda ke wakiltar Borno ta Kudu da majalisar dattawan kasar ta yi.

Rahotanni daga birnin Abujan sun ce tun da sanyin safiyar yau Talata ne ne masu zanga-zangar suka taru a gaban majalisar dokokin dauke da kyallaye da kwalaye da aka yi rubutu a jikin na yin  Allah-wadai da shugaban majalisar dattawan Sanata Bukola Saraki wanda suke zargi da hana ruwa gudu a majalisar.

A makon da ya gabata ne majalisar dattawan Nijeriyan ta sanar da dakatar da Sanata Ndume har na tsawon watanni shida saboda bukatar da yayi na a gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa shugaban majalisar Bukola Saraki na shigo da mota daga waje ba bisa ka'ida ba da kuma Sanata Dino da ke wakiltar jihar Kogi saboda zargin amfani da takardar shaidar digiri na bogi da ake masa.

Cikin 'yan kwanakin nan dai wani adadi mai yawa na al'ummar Nijeriya na ci gaba da nuna rashin jin dadinsu da yadda 'yan majalisar dattawan suke gudanar da ayyukansu biyo bayan kace nace da suke ci gaba da yi da fadar shugaban Nijeriyan lamarin da ya sanya aka fara samun kungiyoyin da suke kiran da a gudanar da zanga-zangogin mamaye majalisar wasu ma suna kiran da a rusa majalisar.