An Fara Kiran Shugaban Afirka Ta Kudu, Jacob Zuma Da Yayi Murabus
(last modified Tue, 04 Apr 2017 16:49:12 GMT )
Apr 04, 2017 16:49 UTC
  • An Fara Kiran Shugaban Afirka Ta Kudu, Jacob Zuma Da Yayi Murabus

Babbar kungiyar kwadago ta kasar Afirka ta Kudu (Cosatu) ta kirayi Shugaban kasar Jacob Zuma da ya sauka daga kan mulki bayan kwaskwarimar da yayi wa majalisar ministocin kasar lamarin da ya kara zafafa rarrabuwan kan da ake da shi a cikin jam'iyyar ANC din mai mulki.

A cikin wata sanarwa da kungiyar kwadagon wacce ta kulla hadaka da jam'iyyar ANC mai mulki din ta fitar ta ce lalle shugaba shugaba Zuma ba shi ne ya dace da shugabantar kasar ba, don haka tana kira gare shi da yayi murabus da barin wani da ya dace ya mulki kasar.

Wadannan kiraye-kiraye da ake yi wa shugaba Zuman da yayi murabus daga mukaminsa ya kara zafi ne bayan korar ministan kudin kasar Pravin Gordhan daga mukaminsa da yayi lamarin da ya kara irin rarrabuwan kan da ke tsakanin jam'iyya mai mulkin, ta yadda hatta mataimakin shugaban kasar Cyril Ramaphosa ya bayyana hakan a matsayin abin da ba za a "amince da shi ba kwata-kwata" ba.

Gwamnatin Zuma din tana ci gaba da fuskantar suka a cikin kasar sakamakon gazawarta wajen magance matsalar tattalin arziki da kasar take fuskanta.