Mali: An kawo Karshen Taron Kasa Na Sasanta Al'ummu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19130-mali_an_kawo_karshen_taron_kasa_na_sasanta_al'ummu
A jiya litinin ne aka kawo karshen taron sasanta al'ummu a birnin Bamaku tare da cimma matsaya akan batun Azwad.
(last modified 2018-08-22T06:59:55+00:00 )
Apr 04, 2017 12:27 UTC
  • Mali: An kawo Karshen Taron Kasa Na Sasanta Al'ummu

A jiya litinin ne aka kawo karshen taron sasanta al'ummu a birnin Bamaku tare da cimma matsaya akan batun Azwad.

A jiya litinin ne aka kawo karshen taron sasanta al'ummu a birnin Bamaku tare da rashin  cimma matsaya akan batun Azwad.

Kamfanin dillancin Labarun Faransa ya ambato cewa; Bayanin bayan taron da aka fitar ya kunshi kira ga dukkanin bangarorin da su ke halarta da su zama masu taka rawa wajen dawo da zaman lafiya a yankunan arewacin kasar da a baya ake kira Azwad.

Shugaban kasar ta Mali Ibrahim Bubakar Keita wanda ya halarci zaman karshe na taron ya ce; Za a kafa kwamiti na kwararru domin yi wata tattaunawar akan yanayin arewacin kasar da ake kira "Azwad"

A cikin watan Maris na 2012 ne kungiyoyin da su ke dauke da makamai kuma masu alaka da alka'ida su ka mamaye yankin arewacin Mali, kafin daga baya sojojin Faransa da Mali su fatattake su.