Mutane Da Dama Sun Rasu Sandiyar Rikicin Kabilanci A Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19136-mutane_da_dama_sun_rasu_sandiyar_rikicin_kabilanci_a_sudan
Rikicin Kabilanci ya yi sanadiyar Mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama a kasar Sudan
(last modified 2018-08-22T11:29:55+00:00 )
Apr 05, 2017 05:33 UTC
  • Mutane Da Dama Sun Rasu Sandiyar Rikicin Kabilanci A Sudan

Rikicin Kabilanci ya yi sanadiyar Mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama a kasar Sudan

Kafar watsa labaran Asharkul Ausat ta habarta cewa da assubahin yau Laraba rikici ya barka tsakanin kabilun Hamar da Kabaabish a jihar Kirdufan ta arewa a kasar Sudan, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane 36 tare da jikkatar wasu 14 na daban.

Rahoton ya ce rikicin ya barke ne bayan da wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kashe wasu Mutane 7 'yan kabilar Kabaabish.

Rikicin dake aukuwa a yankuna uku da mafi yawan arzikin kalkashin kasa na Sudan ke cikin su wato Darfur, Nil-Aby da kuma Kirdufan ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare kuma da raba wasu milyoyi na daban da mahalin su.