Boko Haram Sun kai Hari kan Jami'an Sojin Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19228-boko_haram_sun_kai_hari_kan_jami'an_sojin_najeriya
Wata Majiya a Najeriya ta sanar da kai hari kan tunkar Soja a arewa maso gabashin Najeriya
(last modified 2018-08-22T06:59:56+00:00 )
Apr 07, 2017 13:46 UTC
  • Boko Haram Sun kai Hari kan Jami'an Sojin Najeriya

Wata Majiya a Najeriya ta sanar da kai hari kan tunkar Soja a arewa maso gabashin Najeriya

Sojojin Najeriya hudu ne suna rasa rayukansu a wani harin kwontan bauna da ‘yan kungiyar Boko Haram suka kai ma su a wani kauye da ake kira Gubdori cikin yakin karamar hukumar Dikwa a jihar Borno dake shiyar arewa maso gabashin kasar

Sanarwar da wata majiyar soji ta fitar ta ce mayakan na Boko Haram sun bude wuta da manyan makamai ne akan ayarin motocin soji da ke wucewa a kauyan, yayin da shaidu ke cewa bangaren Abou Mosab Albarnawi na kungiyar ta Boko Haram ne ya kai wannan hari.

A ranar Larabar da ta gabata ma an kai irin wannan hari a yankin karamar hukumar da Dikwai inda aka kashe Mutane 7.