Zanga - Zangar Yin Allah Wadai Da Gwamnatin Kasar Senegal
(last modified Sun, 09 Apr 2017 07:14:12 GMT )
Apr 09, 2017 07:14 UTC
  • Zanga - Zangar Yin Allah Wadai Da Gwamnatin Kasar Senegal

Dubban mutane sun gudanar da zanga-zangar lumana a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal suna rera taken neman sakin fursunonin siyasa da gwamnatin kasar take tsare da su a gidajen kurkuku.

Dubban mutanen da suka fito zanga-zangar da mafi yawansu 'yan adawar siyasa ne sun fito kan manyan hanyoyin birnin Dakar fadar mulkin kasar ta Senegal ne sanye da bakaken kaya suna rera taken yin Allah wadai da bakar siyasar shugaban kasar Macky Sall musamman ta kame 'yan adawar siyasa tare da garkame su a gidajen kurkuku.

Har ila yau masu zanga-zangar sun yi ta rera taken neman sakin fursunonin siyasa daga gidajen kurkuku musamman Khalifa Abubakar Sall tsohon magajin garin birnin Dakar da ake tsare da shi a gidan kurkuku tun a ranar 4 ga watan Maris da ya gabata kan zargin yin sama da fadi da dukiyar kasa, inda masu zanga-zangar suke ganin ana tsare da shi da nufin hana shi tsayawa takara a zabukan kasar masu zuwa.