Shugaban Kasar Mali Ya Nada Sabon Fira Ministan Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19274-shugaban_kasar_mali_ya_nada_sabon_fira_ministan_kasar
Shugaban kasar Mali ya sanar da nadin sabon fira minista a kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:56+00:00 )
Apr 09, 2017 02:45 UTC
  • Shugaban Kasar Mali Ya Nada Sabon Fira Ministan Kasar

Shugaban kasar Mali ya sanar da nadin sabon fira minista a kasar.

A jawabin da ya gabatar ga al'ummar Mali ta hanyar gidan talabijin na kasar a cikin daren jiya Asabar: Shugaban kasar Mali Ibrahim Abubakar Keita ya sanar da sunan ministan tsaron kasar Abdullahi Idrisa Maiga a matsayin sabon fira ministan Mali.

Shugaban kasar ta Mali Ibrahim Abubakar Keita ya kara da cewa: Nada Abdullahi Idris Maiga a matsayin sabon fira ministan Mali ya zo ne bayan amincewa da murabus da Modibo Keita ya yi ne daga kan mukaminsa na fira ministan kasar a ranar Juma'ar da ta gabata.

Nadin Abdullahi Idrisa Maiga a matsayin sabon fira ministan Mali ya zo ne a daidai lokacin da kasar take fuskantar wasu sabbin kalubale a fuskar tsaro musamman ganin yadda 'yan bindiga suke yawaita kai hare-haren wuce gona da iri a sassa daban daban na kasar a cikin 'yan watannin baya-bayan nan.