An Kai Harin Kunan Bakin Wake A kasar Somaliya
Apr 10, 2017 11:21 UTC
Wani dan kunan bakin wake ya tarwatsa kansa a birnin Mogadishu fadar mulkin kasar Somaliya a yau.
Majiyar sojin Somaliya a dazu-duzun nan ta sanar da cewa: Wani dan kunan bakin wake da yayi jigida da bama-bamai ya tarwarsa kansa a sansanin horas da sojin Somaliya da ke birnin Mogadisho fadar mulkin kasar a yau Litinin, inda ya janyo mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu adadi na daban da ba a kai ga sanin yawansu ba.
A jiya Lahadi ma an kai harin kunan bakin wake kusa da tawagar ministan tsaron kasar ta Somaliya Ahmed Muhammad Irfid, inda majiyar tsaron kasar ta bayyana cewa an shirya kai harin ne kan ministan tsaron.
Tags