Fada Ya Sake Barkewa Tsakanin 'Yan Tawaye da Sojojin Sudan Ta Kudu
Sojojin Sudan ta kudu sun kwabza fada da 'yan tawaye a Garin Wau.
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa fadan ya yi tsanani a jiya Litinin tsakanin Dakarun Gwamnatin Sudan ta Kudu da 'yan tawaye a garin Wau, lamarin da ya sanya sama da fararen hula dubu biyu suka nemi mafuka a cikin Coci-Coci.
Rahoton ya ce wasu daga cikin 'yan tawayen sun mamaye gidajen fararen hula a garin na Wau, kuma akalla sun hallaka fararen hula 18 a garin.tun daga shekarar 2013 zuwa yanzu garin na Wau ya fada hanun 'yan tawaye da dama kafin daga bisani Dakarun Gwamnati su kwace shi.
Baya ga wannan rikici, Al'ummar kasar Sudan ta Kudu na fuskantar masifar yiwa, lamarin da ya sanya wasu daga cikin 'yan kasar ke cin ganyayyaki da 'ya'yayen itatuwa domin su rayu, kuma Ma'aikatar lafiyar kasar ta sanar da mutuwar mutane akalla 29 sakamakon bullar cutar kwalara a kasar