Sabon Fira Ministan Mali Ya Sanar Da Sabuwar Majalisar Ministocinsa
Apr 12, 2017 07:21 UTC
Sabon fira ministan Mali ya sanar da sunayen sabbin ministocinsa kwana guda bayan nadinsa a kan mukamin.
Gidan talabijin na France 24 ya watsa rahoton cewa: Sabon fira ministan Mali Abdullahi Idris Maiga ya mika sunayen sabbin ministocinsa ga shugaban kasar Ibrahim Abubakar Keita, inda shugaban kasar ya amince da dukkanin sunayen ministocin a jiya Talata.
Sabuwar Majalisar Ministocin fira ministan Mali Abdullahi Idris Maiga ta kunshi ministoci 35 amma 25 daga cikinsu tsoffin ministoci ne a kasar. Sabuwar gwamnatin Mali dai tana da kalubale a gabanta musamman matsalolin da suka shafi tsaro da na zamantakewar al'umma.
Tags