MDD Ta Yi Galgadi Kan Cutar Kwalara A Somaliya
Ofishin kula da ayikuna jin kai na MDD a birnin Geneva ta ce cutar Amai Da Gudawa ta yi sanadiyar mutuwar Mutane sama da 500
Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa daga birnin Geneva ya nakalto Jens Laerke mai magana da yawun Ofishin kula da ayikuna jin kai na MDD wato OCHA na cewa daga farko wannan shekara zuwa yanzu kimanin Mutane 533 ne suka rasa rayukansu sanadiyar fari da kuma billar cutar Amai da gudawa a kasar Somaliya, kuma matukar Duniya ba ta kai agajin gagguwa adadin mutanan da suka rasa rayukan su na iya karuwa.
A nasa bangare Tarik Jasarevic kakakin Hukumar Lafiya ta Duniya OMS ya ce daga farkon wannan shekara da muke ciki zuwa yanzu kimanin Mutane dubu 25 ne suka kamu da cutar Kwalara a kasar ta Somaliya.
A halin da ake ciki, bayan matsalar tsaro da kasar Somaliyan ke fuskantar sanadiyar hare-haren kungiyar ta'addancin nan ta Ashabab, kasar mai Mutane miliyan 12 na fuskantar fari da kuma cutar kwalara.