Gobara Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane 22 A Senegal
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i19412-gobara_ta_yi_sanadiyar_mutuwar_mutane_22_a_senegal
Tashin gobara a wajen wani taro na Al'ummar musulmi a yankin Medina Gounas na kasar Senegal ya yi sanadiyar mutuwar mutane 22 tare da jikkata wasu sama da 80 na daban.
(last modified 2018-08-22T11:29:57+00:00 )
Apr 13, 2017 18:55 UTC
  • Gobara Ta Yi Sanadiyar Mutuwar Mutane 22 A Senegal

Tashin gobara a wajen wani taro na Al'ummar musulmi a yankin Medina Gounas na kasar Senegal ya yi sanadiyar mutuwar mutane 22 tare da jikkata wasu sama da 80 na daban.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya habarta cewa gobarar ta tashi ne a wannan Alkhamis a garin Tambacounda dake kudu masu gabashin yankin Medina Gounass, inda a ko wata shekara Al'ummar musulmi mabiya darikar tijjaniya na kasar Senegal, Guinee da kuma sauran kasashen yammacin Afirka ke taruwa domin gudanar da wani taron Darikar mai suna Daka.

Ya zuwa yanzu dai ba a kai ga gano musababin tashin gobarar ba.