Yau Ake Zaben Shugaban Kasa A Jamhuriya Benin
Yau Lahadi al'umma kasar Benin milyan hudu da dari bakwai da suka tantanci zabe ke kada kuri'a a zaben shugaban kasa.
'Yan takara 33 ne da suka hada da mata biyu ke fafatawa a zaben na yau domin maye gurbin shugaban kasar mai barin gado THOMAS BONI YAYI, wanda ya kammala wa'adin mulkin sa na biyu.
Mr Boni dai baya daga cikin 'yan takara dake neman shugabancin kasar a wannan karo, kasancewar kundin tsarin mulkin kasar ya haramta masa yin hakan bayan yin wa'adi biyu na shekaru biyar-biyar.
Tun da farko dai an shirya yin zaben ne a ranar 26 ga wtan Fabrairu daya gabata saidai aka jinkirta zaben har zuwa 6 ga watan Maris saboda tsaiko da aka samu wajen sarafa katinan zaben dama raraba su ga wadanda suka tantanci zaben.
Daga cikin 'yan takaran, biyar ne dai ake ganin zasu iya fiddo kai a ruwa, wandanda suka hada da firaministan kasar mai barin gado Lionel Zinsou, da wasu mayan attajiran kasar biyu Patrice Talon da Sebastien Ajavon sai kuma wasu ma'aikatan bankuna an kasa da kasa biyu da suka hada da Abdulaye Bio Tchane da Pascal Irenee Koupaki.