Mali : MDD Ta Yi Kira A Kan Aiwatar Da Yarjejeniyar Zaman Lafiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i1948-mali_mdd_ta_yi_kira_a_kan_aiwatar_da_yarjejeniyar_zaman_lafiya
Wakilan kasashe 15 mambobin kwamitin tsaro na MDD dake ziyara a Mali sunyi kira akan gaggauta aiwatar da yarjejeniyar zamen lafiya a wannan kasa ta Mali.
(last modified 2018-08-22T06:57:56+00:00 )
Mar 06, 2016 03:01 UTC
  • Mali : MDD Ta Yi Kira A Kan Aiwatar Da Yarjejeniyar Zaman Lafiya

Wakilan kasashe 15 mambobin kwamitin tsaro na MDD dake ziyara a Mali sunyi kira akan gaggauta aiwatar da yarjejeniyar zamen lafiya a wannan kasa ta Mali.

tawagar wace ta isa Mali a ranar juma'a data gabata ta gana da firaministan kasar a jiyya Asabar, kafin daga bisani ta isa biranen Mopti dake tsakiya da kuma Tumbuktu dake arewa maso yammacin kasar inda ta samu ganawa da dukkan bangarorin da batun ya shafa.

wannan dai na zuwa ne a kasa da makwanni uku kafin babban taron sulhu a arewacin kasar ta Mali.

A cewar MDD abun yi na farko shi ne aiwatar da yarjejeniyar ta zamen lafiya yadda ya kamata.

wani batu kuma da aka maida hankali akan sa shi ne yadda zamen lafiya ya kasa samun gindin zama watanni 9 bayan sanya hannu kan yajejeniyar sulhu tsakanin gwamnatin kasar da 'yan tawaye a wtan Yuli shekara data gabata.