An Hallaka 'Yan ta'addar Ashabab A Somaliya
Wata Majiyar tsaron Somaliya ta sanar da hallakar yan ta'addar Ashabab biyu a Magadushu babban birnin kasar
Ministan Tsaron cikin gidan na kasar Muhamad Aslou ya tabbatar da wannan labari a wannan Litinin, inda ya ce bayan hallaka 'yan ta'addar, jami'an tsaron kasar sun samu nasarar tarwatsa wata Mota dake shake da bama-bamai ta 'yan ta'addar.
Ministan tsaron cikin gidan ya kara da cewa lamarin ya faru ne a yayin da 'yan ta'addar na kungiyar Ashabab ke shirin kai wasu jerin hare-haren ta'addanci kan Al'ummar birnin na Magadushu.
A nasa bangare, Ahmad Harsi babban jami'i tsaro a kasar ya sanar da hallaka wani komandan mayakan Ashabab a yankin Jubaland dake kalkashin kungiyar ta Ashabab a kudancin kasar.
Ya zuwa yanzu dai Dakarun wanzar da zaman Lafiya na kasashen Afirka wato Amison tare da hadin gwiwar Dakarun kasar ta Somaliya sun samu nasara mai yawa a yakin da suke yi da kungiyar Ashabab a kasar ta Somaliya, amma har yanzu kungiyar na ci gaba da kai hare-haren ta'addanci a kasar.