Shugaban Afirka Ta Kudu Ya Ce Ba Zai Yi Murabus Ba
(last modified Tue, 18 Apr 2017 06:37:45 GMT )
Apr 18, 2017 06:37 UTC
  • Shugaban Afirka Ta Kudu Ya Ce Ba Zai Yi Murabus Ba

Shugaban kasar Afirka ta kudu Jacob Zuma ya jaddada cewa ba zai yi murabus daga kan shugabancin kasar ba sakamakon matsin lambar jam'iyyun adawar siyasa na kasar.

Kamfanin dillancin labaran Xin Huwa ya bayar da rahoton cewa, a lokacin da yake gabatar da wani jawabi a gaban dubban magoya bayansa a birnin Durban na kasar Afirka ta Kudu, shugaba Zuma ya bayyana cewa, makomarsa tana a hannun ra'ayin masu rinjaye a kasar Afirka ta kudu.

Tun bayan garambawul da shugaba Zuma ya yi wa majasar ministoci a karshen watan Maris da ya gabata, da hakan ya hada da sauke ministan kudi na kasar Parvin Gorghan daga kan mukaminsa, yake ci gaba da fuskkantar matsin lamaba daga jam'iyyun adawa, da ma wasu daga cikin 'yan jam'iyyarsa ta ANC.